Stephanie News, Dell USB Drivers, Android Devices, Charging, Apple, Nokia Flash File, Samsung Galaxy

Minggu, 07 Agustus 2016

DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO

DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO - with the rapid development of today's technology we must enrich our knowledge of gadgets, because every day there are many new gadgets that are made with advantages, in blogs Stephanie News we will meriview many gadgets from various brands ranging from the specification and its price .. Now we will discuss first about DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO please see our explanation to finish:

Articles : DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO
full Link : DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO
Article Hausa,

You can also see our article on:


DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO



BISMILLAHI..
 
A wannan karon ne akayi labarin tunawa da Sardaunar Saokoto Sir Ahmadu Bello da Kuma TAfawa Balewa Firemiyar Nigeria na farko. Shekaru Hamsin kenan da kashesu Allah ya jikansu. 

Idan na Kalli Nigeriya tambayoyi da yawa suna zuwa zuciyata, Mutanen Nigeriya suna son tunawa da mutanen kirki irin su sardaunar amman kuma mun gaza wajen koyi da halayensu. Mafi yawan lokaci ina tambayar kaina da ace wanda ya rasu zai iya dawowa me zai faru idan Sardauna ya dawo; me zai faru idan Tafawa Balewa ya dawo? Me zai faru idan Namandi Azikwe ya dawo; me zai faru idan Awolowo ya dawo?  Me zai faru idan mutane irin su Murtala Muhammad zasu dawo da sauran dai Mutanen kirkin Nigeria da akayi gwagwarmaya dasu.
Babu abin da zasu zo su tarar sai dai suzo suga mutanen da suka bari basu da hadin kai, zasu zo su tarar Arewacin Nigeria zaman lafiya yayi mata karanci. Zasu zo su rashin cin hanci da rashawa shine kan gaba a kasar amman kuma mafi yawan jaridun kasar basa buga labarin. Me yasa? Saboda basu suke juya akalar Jaridun ba.
A yanzu da nake muku Magana kasashen Afrika da dama basa zaman lafiya. Me zai faru idan wadannan mutanen kirkin suka dawo? Zasu zo su tarar muna yaki da junanmu, zasu zo su tarar mutane Nigeria suna siyo abin da suke da arzikinsu a cikin kasar kuma suna siyar da abin da basu dashi (Misali fetur). Zasu zo su tara da Yan Nigeriyan da basu son Kasarsu kuma basa son junansu. Zasu zo su tarar da Yan Nigeriyar da su su sardaunar suka sha gwagwarmaya don kada su zama bayin turawa, wannan karon da kansu yan Nigeriyan suke zuwa kasashen turawar don suyi bauta.

Zasu zo su tarar da yan Nigeria wanda basa alfahari da al’adarsu, kabilarsu ko kuma abubuwan da suka kera. Zasu zo su tarar da Yan Nijeriyan da zasu bude kamfani a cikin kasar amman sais u dinga sanya ma abin da suke kerawa Made in China (Wato anyishi daga China). Hatta Abinci yana da sunan turawa. Idan muka noma dankali sai muce masa Dankalin Turawa koda kuwa a Kudan ta jihar kaduna aka nomashi. Idan mun hada biredi da kosai sai muce masa sandswitch. Wannan sune yan Nigerian da zasu zo su tarar.
Za kuma suzo su tarar da Yan Nijeriyan da baza fadin labarin kansu kuma basa damuwa da jin labarin kansu; hatta gidajen jaridu sai dai su kalli CNN, Radio France, BBC, Aljazeera da sauransu bayan muna dasu NTA, Radiyoyin Jiha, Jaridun trust da sauransu. Zasu zo su tarar da yan Nijeriyan da basa jin dadin kansu. Idan suna son yin Nishadi sai dai dai su Kalli Manchester United, Real Madrid, Arsenal, Barcelona bayan muna dasu Kano Pillars, Rangers, Eyimba da sauransu.
Za kuma suzo su tarar da yan Nijeriyan da basu damuwa da wakokin gargajiya sai dai su mayar da hankalinsu wajen su 2pack, Shakira, Lil wayne da sauransu.
Me yasa bama tunama kanmu da wadannan abubuwan na Zahiri ne? Hatta rashin Lafiya dan Adam yake yi sai ya tafi America, Germany, USA bayan muna da manya manyan asibitoci. Indai baza mu canza ba babu inda zamu. Indai mun kasa tunani har abada baza mu canza ba.
Muna da manyan Jami’oi amman yaran masu kudi sai dai akaisu wata kasar. Muna da injiniyoyi amman manyan hanyoyinmu da gadojinmu duk yan China ne ke yinsu. Hakan yana nufin injiniyoyinmu ko hanya baza su iya yiba kenan? Muna da likitoci amman wasu daga yan siyasa da masu kudi da sunji suna rashin lafiya to ya danganta ne da kasar da mutum yake zuwa hutu. Idan kana zuwa hutu ingila ne sai kaje London, idan kana zuwa Spain ne sai kaje Madrid don kawai a duba lafiyarka. Hakan yana nufin bamu da imani akan akan likitocinmu kenan.
Manyan shugabanninmu sun kirkiro da hanyar ilimi kyauta amman suna daukar yaransu suna karatu a kasar waje. Hakan yana nufin su kansu basu yarda da makarantarmu ba kuma sun kasa gyarawa.
To Allah dai ya kyauta. Gashi muna son mu dinga tunawa da yan mazan jinya amman mu kanmu bamu yarda da kawunanmu ba. Mu kanmu bamu shaidar junanmu haka abin yake akan shagabanninmu.

ALHAMDULILLAHI....

 07035311650
SHARE AND COMMENT...



we feel the information DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO that's all.

hopefully the information DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO that we have conveyed can provide benefits for you and all visitors of this blog, if any criticism and suggestions please comment.

you just read DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO if this article is considered useful and you want to bookmark and share it please use the link https://stephaniefulke.blogspot.com/2016/08/da-ace-su-sardauna-da-ire-irensu-zasu.html and what if you want other information look for another page in this blog.

Tag : ,
Share on Facebook
Share on Twitter
Share on Google+
Tags :

Related : DA ACE SU SARDAUNA DA IRE-IRENSU ZASU DAWO

  • El-Rufa'i ya haramta addinin Shi'a a Jihar KadunaBismillahi..Gwamnatin jihar Kaduna a Nigeria ta haramta dukkan aikace-aikacen kungiyar 'yan uwa Musulmi ta 'yan Shi'a mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.Mai magana da yawu ...
  • Abubuwan da ya kamata ka sani a WhatsappBismillahi..YADDA AKE GYARA RUBUTU DA SAKE MASA FONTS STYLE TA WHATSAPP ```Assalamu Alaikum```_Kamar yadda mutane da yawa suke ta tambaya, ta yaya za su yiwa rubutunsu k ...

0 komentar:

Posting Komentar